Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Wayi Gari Da Sabon Ango Tinubu


Sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya a daidai lokacin da manazarta ke cewa ana fuskantar kalubalen da ba'a taba ganin irinsa ba a kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka, yayin da wasu ‘yan kasar ke fatan samun rayuwa mai inganci, wasu kuma na shakkun gwamnatin za ta yi aiki fiye da ta baya.

Dubban 'yan Najeriya da wasu shugabannin gwamnati ne suka halarci bikin rantsar da Tinubu mai shekaru 71 a duniya a Abuja babban birnin kasar.

Tinubu ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a jagoranci kasar da a shekarar 2050 aka yi hasashen za ta zama kasa ta uku a yawan al'umma a duniya, wacce za ta yi kunnen doki da Amurka bayan Indiya da China.

Tinubu tsohon gwamnan jihar Legas ne, wadda ita ce cibiyar tattalin arzikin Najeriya, ya yi alkawarin ci gaba da kokarin da Buhari ke yi na samar wa ‘yan kasa ribar dimokuradiyya a kasar da ke fama da munanan tashe-tashen hankula na tsaro da fatara da yunwa da suka jefa mutane da dama cikin takaici da fushi.

Kuma kasancewar har yanzu jam’iyyun adawa na ci gaba da fafatawa a gaban kotu kan nasarar zaben, Tinubu ya kuma yi alkawarin sake hada kan kasar.

A jawabinsa na farko a matsayinsa na shugaban kasa, Tinubu, wanda kuma dan jam’iyyar Buhari ne, ya bayyana cewa, “fatan Najeriya ya dawo” kuma ya ce zai yi aiki fiye da inganta tattalin arziki da tsaro domin hada kan al’ummar da ke fama da rarrabuwar kawuna da kuma tabbatar da adalci ga kungiyoyin da ke rikici da juna.

"Mun jure wahalhalu da zai sa wasu al'umma su durkushe," in ji Tinubu. "Manufarmu ita ce mu inganta hanyoyinmu ta hanyar da za ta ciyar da bil'adama, karfafa tausayi ga juna da kuma ba da lada ga kokarinmu na hadin gwiwa."

Alamar mika mulki da biyayya ga sabon shugaban kasa, Janar Lucky Irabor, babban hafsan hafsoshin Najeriya, ya mika wa Buhari tsofaffin tutocin kasa da na tsaron Najeriya, ya kuma karbi sabbi daga Tinubu, wanda kuma shi ne babban kwamandan sojin kasar.

Bayan zaben kasa da aka yi a watan Fabrairu, sabbin zababbun gwamnonin jihohi ma sun yi rantsuwar kama aiki a jihohin Najeriya da dama a ranar litinin.

XS
SM
MD
LG