Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Tsallake Rigingimu Da Dama Bata Wargaje Ba, Inji Yusuf Maitama Sule


Shugaban Huumar Zabe da Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule a hannun dama, a shekarar 2011
Shugaban Huumar Zabe da Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule a hannun dama, a shekarar 2011

Babban ci gaban da Najeriya ta samu tun kafin ma ta samu mulkin kai shi ne yadda ta tsallake wargajewa daga rigingimun da ta fuskanta ta ci gaba da kasancewa kasa daya.

Inji Alhaji Yusuf Maitama Sule kasar ta fada cikin rigingimu da yawa da ake zaton daga nan kasar zata wargaje amma bata wargaje ba.

Batun samun mulkin kai da 'yan kudu suka so a samu a shekarar 1952 da arewa tace a dan bada karin lokaci bai yiwa mutanen kudu dadi ba. An bisu a hankali har aka samu masalaha da kudancin kasar.

A shekarar 1957 zuwa 1958 an samu rikici akan kidayar yawan mutane kasar. Amma Allah Ya taimaka kasar ta sallake rijiya da baya.

Zaben 1959 bai ba wata jam'iyya yawan kuri'un da zata kafa gwamnati ba duk da cewa NPC, jam'iyyar arewa ita ce ta fi yawan kujeru.Dole sai an hada da wata jam'iyya a iya kafa gwamnati.

An samu wasu da suka ce jam'iyyun NCNC da AG su hadu su kafa gwamnati amma masu hankali suka ce yin hakan tamkar ware arewa ne wadda ta fi yawan kujeru kuma arewa na iya tunanen ballewa daga kasar. Da aka daidaita ne NPC da NCNC suka kafa gwamnati. A nan ma kasar ta sake tsallake rijiya da baya.

Zaben 1964 ya jawo rarrabuwar kawuna inda jam'iyyun NCNC da AG suka ki shiga zaben. Sai NPC da kawarta UNDP suka shiga zaben suka ce sun ci. Dr. Nnamdi Azikiwe shi ne shugaban kasa amma yace ba zai kira a kafa gwamnati ba. Rikici ya tashi kasar tana nema ta ruguje. A wannan rikicin ma kasar ta tsallake rugujewa.

Sai 1965 da za'a yi zaben yankin yammacin kasar aka soma kone-konen gidaje da mutane, kasar ta zama kamar zata ruguje. Wannan rikicin ya kaiga hambarar da gwamnatin farar hula ta farko a kasar yayinda sojoji suka yi juyin mulki.

Bayan an yi yaki na kusan tsawon shekaru uku kasar ta sake dawowa ta zama daya tare da yafewa juna.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG