Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Allah Wadai Da Juyin Mulkin Mali


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin dadi game da juyin mulkin da sojoji suka yi wa tsohon shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita a jiya Talata.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin twitter.

"Mun yi kiran da a dawo da tsarin mulkin dimokradiyya cikin gaggawa a Mali," a cewar ministan.

Sojojin da suka yi juyin mulki sun jaddada cewa sun shirya zabe nan ba da dadewa ba don mayar da kasar akan turbar dimokradiyya.

Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na ci gaba da bayyana matsayinsu bayan da sojoji suka bada sanarwar kifar da shugaban kasar.

Kakakin sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali Kanar Ismael Wague ya bayyana dalilinsu na aikata hakan a kafar television mallakar gwamnatin kasar Mali dauke da sanarwar kwamitin CNSP.

"Ya ku 'yan Mali maza da mata, an sha kona kauyuka sukutum ana ta kashe bayin Allah a kasarmu, tsoro da firgita sun mamaye zukatan ‘yan Mali, haka kuma ‘yan Mali sun zama ‘yan gudun hijira a cikin kasarsu," a cewar Wague.

Wasu sojojin kasar Mali
Wasu sojojin kasar Mali

Ya cigaba da cewa, "Sata da fashi da ta’addanci sun bata zumuncin dake tsakanin jama’a, ga rashin mulki na gari, shi ne dalilinmu na yin hakan."

Yanzu dai sojojin da suka yi juyin mulkin na jiya Talata sun yi kira ga kungiyoyin kwadago da na ci gaban al’uma da jam’iyun siyasa su guji dukkan abubuwan da ka iya tayarda hatsaniya.

Ita kuwa kungiyar CEDEAO ta bada sanarwar dakatar da kasar ta Mali daga sahun mambobinta tare da rufe iyakokin kasashe makwabtanta da nufin nuna rashin jin dadinta game da wannan juyin mulki da ya bada damar tsare shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Frai ministansa Boubou Cisse a barikin sojan Kati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG