Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Zama Kasa Ta Uku a Afrika Da Yawan Masu Dauke Da Coronavirus


A cikin sababbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar NCDC, mutanen da su ka kamu ya sauka da mutum 241 a cikin sa'o'i 24 da su ka gabata, wanda hakan ya mayar da adadin ma su cutar zuwa 10,819 a kasar.

Najeriya ta zama kasa ta uku a Afrika da yawan ma su dauke da cutar coronavirus bayan kasashen Eygpt da Afrika ta Kudu.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan ma su dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabbin kamuwa 142.

Sauran jihohin sun hada Oyo (15), Birnin tarayya Abuja (13), Kano (12), Edo (11), Delta (10), Kaduna (9), Rivers (9), Borno (8), Jigawa (4), Gombe (3), Plateau (3), Osun (1), Bauchi (1).

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 10,819 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 3,239 suka samu lafiya, sai kuma mutane 314 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG