Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Nazarin Sabbin Dabarun Sadarwa Wajen Yakar Ta'addanci


Sojojin Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri
Sojojin Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri

Najeriya zata hada kai da Britaniya da Amurka wajen bullo da sabuwar dabarar da nufin tallafawa matakan sojan da ake dauka wajen yakar ta'addanci da 'yan tsagera

Najeriya tana shirin daukar sabbin matakan sadarwa na dakile irin ra'ayoyin tsageranci da wasu ke bazawa ta hanyar mamaye kafofin sadarwa da ra'ayoyin sassauci da zamantakewar al'umma cikin lumana.

Jami'i mai kula da ayyukan soja na Britaniya a Najeriya, Kanar John Fletcher, yace ba wai za a yi amfani da wannan dabara wajen yin wa'azi ko fadawa 'yan Najeriya yadda zasu yi ba ne, za a yi amfani da irin kwarewar da suek da ita ne wajen kirkiro dabara mai nagarta ta yaki da tsageranci.

Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaron kasa, Kanar Sambo Dasuki, ya fada a gaban wani taron bitar da aka yi a Abuja kan “Dabarun Sadarwa Wajen Yakar Ta'addanci” cewa ana bukatar irin wannan dabarar a saboda matakan soja kawai ba zasu iya kawar da ta'addanci ba.

Kanar Dasuki ya bayyana wannan sabuwar dabara a zaman ta karfafa hulda da jama'a da nufin murkushe akidar nuna gabar da tsagera ke yadawa.

Yace irin wadannan muhimman dabarun sadarwa su na da matukar muhimmanci ga kokarin gwamnati na kawar da ta'addanci, kuma za a ci gaba da tsara su da yi musu garambawul daidai bukata domin dacewa da irin halin da ake ciki.

Yau shekaru biyu ke nan Najeriya tana amfani da sojoji da sauran jami'an tsaronta wajen yakar 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar. Mahalarta wannan taron bita kusan baki dayansu sun yarda cewa yin amfani da karfin soja ba zai murkushe ta'addanci a Najeriya ba.

Mahalarta taron suka ce duk da cewa matakan soja sun haifar da wani ci gaba, akwai bukatar gabatar da wasu sabbin matakan da zasu kawar da ra'ayoyi ko akidoji na tsageranci.
XS
SM
MD
LG