Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Wadansu 'Yan Bindiga Sun Kashe Maharba Shida


Kamar yadda rahotanni da kuma shaidun gani da ido su ka bayyana, wadansu mahara akan rakuma sun yi dirar mikiya a garin Aljannaru da ke da tazaran kilomita 35 daga garin Song a jihar Adamawa a Najeriya, inda su ka lalata amfanin gona da kuma yiwa wasu mata fyade tare da kashe wasu ‘yan sakai na marhaba su shida da su ka kai dauki.

Maharan na dauke da muggan makamai da kuma manyan bindigogi wanda kawo yanzu ba'a san ko makiyaya ne da ke wucewa ba ko kuma mayakan Boko Haram ne su ka sauya salo.

Wani daga cikin shugabanin hadakar kungiyar ‘yan sakai na maharba a jihar Adamawan, ya ce sun kadu da kisan da aka yiwa maharban su to amma ba gudu ba jada baya a taimakon da su ke yi.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Yahaya Suleiman, ya tabbatar da faruwar wannan al’amari, inda ya ce tuni aka dauki mataki game da kwararar irin wadannan ‘yan bindiga.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da jama'a ke kasa barci sakamakon matsalar tsaro da suka hada da masu garkuwa da jama'a da bayanai ke cewa sun kafa sansanoni akan wasu duwatsun jihar.

A cikin kwanakin nan da su ka gabata gwamnatin jihar Adamawa ta sayo wasu motoci da baburan hawa da nufin taimakawa hukumomin tsaro, koda yake kawo yanzu ‘yan sakai na maharba da sauran kungiyoyin sakan ba'a tuna da su ba.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu Ibrahim Abdulaziz daga Jalingo:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG