Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Yau shekaru hamsin ke nan da aka yi juyin mulkin farko


Sardauna Sir Ahmadu Bello da wasu shugabannin Najeriya a London shekarar 1957
Sardauna Sir Ahmadu Bello da wasu shugabannin Najeriya a London shekarar 1957

Ranar 15 watan Janairun shekarar 1966 sojoji suka yi juyin mulkin farko suka kashe Sardauna da Tafawa Balwa da wasu shugabannin siyasa da manyan sojoji 'yan aslin arewacin Najeriya

Yayinda yake zantawa da Muryar Amurka Alhaji Maitama Sule tsohon minista a gwamnatin Abubakar Tafawa Balewa ya bayyana dalilin da ya sa aka yi juyin mulkin.

Yace duk da an samu wasu miskiloli saboda hali irin na rayuwa Najeriya ta taso da kwarjini da mutunci a idon duniya da kasaita kuma tattalin arzikin kasa yana tafiya daidai gwagwado.

Yace rayuwa a fadi ne a tashi. Ana tafe hakan amma kasashen duniya suna ganin girman Najeriya. Wajen kwanaki biyu kafin juyin mulkin a Najeriya aka yi taron kungiyar kasashen da ingila ta raina, kungiya da a lokacin tana gap da rugujewa. Najeriya ce ta taimaka lamura suka jaru.

Juyin mulkin farko ya raba kasar da shugabanci irin na su Abubakar Tafawa Balewa, Sardauna da su Azikiwe da sauransu.

A lokacin duk duniya ta yadda cewa akwai kasashe uku masu tasowa wadanda idan shugabanninsu suka yi shekaru 15 ko 20 suna shugabanci zasu bunkasa su kamo kasashen da suka cigaba.

Amma tun daga lokacin da aka kawar da shugabancin abubuwa basu yiwa kasar daidai ba. A wancan zamani akwai zumunci da mutunci da adalci da rashin zalunci da kamanta gaskiya da son kasar fiye da son kai suke gaban shugabannin lokacin.

Wasu sun ce zalunci da cin hanci ya sa aka kawar dasu amma da Nzegwu wanda ya kashe Sardauna ya ga takardun bakin sa ya ga cewa ma bashi ake binsa sai da yayi nadamar kasheshi. Tafawa Balewa bashi da kwabo daya na ajiya a banki.Dukansu babu mai gidajen haya ko motocin sufuri ko kamfanoni ko hannun jari a wasu kamfanoni. Babu kuma mai rijiyar mai duk da cewa shi Maitama Sule ne ministan mai na lokacin. Gidajensu na kansu na kasa ne da aka yi masu kwaskwarima da siminti

Sardauna shi ne shugaban jam'iyyar dake mulkin Najeriya amma ya ki karban shugabancin kasar ya bar ma Tafawa Balewa.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG