Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fargabar Yiwuwar Samun Ambaliyar Ruwa Mai Tsanani A Najeriya


Ambaliyar Ruwa a Najeriya.
Ambaliyar Ruwa a Najeriya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce kimanin mutum 600 ne suka mutu, yayin da miliyan uku ambaliyar ta shafa  a jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriya a bara.

A baya dai an samu ruwan sama sosai a Najeriya tsakanin watan Yuni da Oktoba a shekarar da ta gabata, kuma kasar ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru goma, lamarin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya kashe mutum sama da 600 tare da raba kimanin miliyan 1.4 da muhallansu.

Barazanar ruwan sama kamar da bakin kwarya, za ta iya yin illa ga al'ummomi masu rauni, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, musamman wadanda har yanzu ke fama da illar ambaliyar ruwan bara.

Ambaliyar ruwan da ta auku a shekarar da ta gabata, ta samo asali ne sakamakon ruwan sama da ba a taba ganin irinsa ba, hade da fitar da ruwa mai yawa daga madatsar Lagdo da ke Arewacin Kamaru.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce kimanin mutum 600 ne suka mutu, yayin da miliyan uku ambaliyar ta shafa a jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriya a bara.

Yanzu haka dai hukumar ta NEMA na gargadin yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a fadin kasar nan da watanni masu zuwa.

Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Matthias Schmale, ya ce matsalar sauyin yanayi ce ke da alhakin haka, kuma dole ne hukumomi su inganta samar da kudaden da ake kashewa kan kayayyakin more rayuwa.

Idan aka sami karin tallafi da wayar da kan jama'a game da matsanancin yanayi, hukumomi na fatan rage tasirin ambaliya a Najeriya a wannan shekara.

XS
SM
MD
LG