Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Hadu Da Tunisia, Egypt Da Ivory Coast


Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau

A ranar Lahadi za a buga wasan na Najeriya a filin wasa na Garoua da ke Kamaru mai karbar bakuncin gasar.

‘Yan wasan Najeriya na Super Eagles za su hadu da Tunisia a zagayen ‘yan 16 bayan da suka kammala zagayen rukuninsu cikin annashuwa.

Najeriya ta lashe dukkan wasanninta uku inda ta kare da maki tara bayan da ta doke Egypt da ci 1-0, Sudan 3-1 da Guinea-Bissau da ci 2-0 a rukunin D.

A ranar Lahadi za a buga wasan a filin wasa na Garoua da ke Kamaru mai karbar bakuncin gasar.

Tunisia ta kare a matsayi na uku a rukuninsu na F amma ta yi nasarar tsallakawa rukunin na ‘yan 16.

Ita dai Tunisia ta fuskanci kalubale da dama a wannan gasa ta AFCON 2021, a wasanta na farko ta sha kaye da 1-0 a hannun Mali kafin ita ma ta yi wa Mauritania cin kaca da ci 4-1 a wasanta na biyu.

Sai dai ta sake shan kaye a hannun Gambia a wasanta na uku da ci 1-0, kuma gab da wasan ne kusan rabin ‘yan kwallonta suka kamu da COVID-19.

Ita kuwa Egypt da ta zo ta biyu a rukunin D, za ta hadu da Ivory Coast ne a ranar Laraba a filin wasa na Japoma da ke birnin Douala.

.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG