Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Iya Kera Motoci 400,000 A Duk Shekara- NADDC


Kamfanin kera motoci a Najeriya
Kamfanin kera motoci a Najeriya

Kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya sun zuba jarin sama da Naira Biiyan 500 don inganta ayyukan hukumar NADDC

A kokarin da hukumar da ke sa ido wajen ci gaba da zane-zanen motoci ta kasa a Najeriya wato NADDC a takaice, manyan kamfanonin kera motoci a ciki da wajen kasar sun hada hannayen jari na kudi sama da Naira biliyan dari biyar don kafa wata masana’anta da za ta taimaka wajen ci gaban humakumar.

Kamfanonin sun hada da Dangote-SinoTrucks, Innoson, PAN, Cherry, Peugeot, Stallion Group, Hyundai, Honda, Elizade, Lanre Shittu, JAC, Kojo, Nord, Omaa, Vistar, Jet Systems, National Trucks Manufacturers, GAC, Kia, Mikano/Geely.

Kamfanin kera motoci a Najeriya
Kamfanin kera motoci a Najeriya

A makon jiya ne Babban Daraktan hukumar ta NADDC Malam Jelani Aliyu tare da tawagarsa suka kai ziyara a wadannan kamfanoni don duba ayyukansu, kuma a yanzu haka kamfanonin ne ke sahun gaba wajen kera motoci da kuma sayar da su a Najeriya, kana suna da kwarewar kera sama da motoci 400,000 a duk shekara

Kazalika kwarewarsu bai tsaya ga kera motocin da ke amfani da burbushin mai kadai ba har motocin da ke amfani da wutar lantarki.

A ci gaban da Najeriya ta samu yan’kwanaki da suka gabata kasar ta soma amfani da motocin da ke amfani da wutar lantarki kirar kamfanin Hyundai Kona Ev da kuma gwaji da aka yi na babban motar daukar kaya dake amfani da wutar lantarki duk na kamfanin.

Kamfanin kera motoci a Najeriya
Kamfanin kera motoci a Najeriya

A takaice dai hukumar ta NADDC za ta iya kera motoci dubu 400 a duk shekara. Abin da kasar ke bukata kawai shi ne wadanda za su sayi motocin da za’a rika kerawa a kasar fiye da kashe makudan kudade wajen shigo da motocin da aka taba amfani da su a ka kuma yi gwanjonsu a kasashen waje.

XS
SM
MD
LG