NIAMEY, NIGER —
A shirin Nakasa na wannan makon za mu fara da bankwana ne da Fatima Mali mai aikin waye kai da ba da horon sana’oin hannu a jihar Maradi.
Sannan mu leka Jihar Bauchi inda Nakasassu ke fama da matsalar rashin samun aikin yi duk kuwa da cewa da dama daga cikinsu sun yi karatu zuwa matakin difloma.
Haka kuma wadanda suka dogara da sana’oin hannu don kare kansu daga kaskanci ko bara ba sa samun ciniki kamar yadda ya kamata na biyan bukatunsu.
Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna