Accessibility links

Namadi Sambo Ya Bukaci Kotuna Su Bi Kaidar Aiki

  • Halima Djimrao

Mohammed Namadi Sambo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Namadi Sambo ya furta haka ne da yake kaddamar da babbar kotun tarayya a Lafiya, jahar Nassarawa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci alkalai da lauyoyi da su tabbatar da bin k’a’idojin aikin su sau da kafa don tabbatar da gudanar da aikin su yadda ya kamata. Mataimakin shugaban kasar Najeriya Mohamed Namadi Sambo ne yayi wannan furuci a lokacin da yake kaddamar da babbar kotun tarayya a garin lafiya jahar Nassarawa. Babban jojin kotun tarayya, Ibrahim Auta da gwamnan jahar ta Nassarawa Umaru Tanko Almakura su ma sun yi muhimman bayanai kamar yadda za ku ji a cikin rahoton da wakiliyar Sashen Hausa a yankin, Zainab Babaji ta aiko daga birnin Lafiya, jahar Nassarawa:

XS
SM
MD
LG