Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Ba Da Jimawa Ba Za A Hallaka Bello Turji - Gwamnan Zamfara


Dauda Lawal
Dauda Lawal

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana yakinin cewar nan bada jimawa ba ta’addancin da kasurgumin dan ta’addan nan daya jima yana aikatawa a jihar da kwayenta zai zo karshe.

Gwamna Lawal ya sake jaddada aniyar ganin cewa nan da dan lokaci kadan za a kama ko hallaka jagoran ‘yan ta’addar.

Lokacin da aka tambayeshi game da yiyuwar dakatar da ayyukan kasurgumin dan bindigar a cikin shirin siyasar tashar talabijin ta Channels me suna “Politics Today” a jiya Litinin, gwamnan yace “lokaci kawai ake jira”.

“Da irin wannan tsari da muke da shi a kasa, na hadin gwiwa tsakaninmu (gwamnatin jiha) da ta tarayya da hukumomin tsaro, ina baku tabbacin cewar, lokaci kawai ake jira; amma za a hallaka Turji nan da lokaci kadan.”

Kalaman gwamnan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da dakarun sojin Najeriya suka samu gagarumar nasara akan ‘yan bindiga, inda suka hallaka dan bindigan da aka jima ana nema Halilu Sububu, wanda ya addabi al’ummar jihohin Zamfara da Sokoto da sauran sassan arewa maso yamma.

A makon da ya gabata an hallaka Halilu Sububu da fiye da ‘yan bindiga 30.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG