Ruftawar gadar Tatabu, wacce ta hada kudancin Najeriya da yankin arewa maso yammacin kasar, ya shafi gadar jirgin kasa dake Tatabun, al’amarin da yasa yanzu samada mako biyu babu zirga zirgar jiragen kasa daga Legas zuwa Kano.
Amma Ministan sufuri Rotimi Ameachi, ta bakin kakakin hukumar zirga zirga jiragen kasa na Najeriya Alhaji Yakubu Mahmud, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Babangida Jibril cewa, cikin dan kwanakin nan za’a kammala aikin gayaran gadar.
Tunda farko Ministan Sifirin Rotimi Ameachi wanda yayi magana kan wannan gadar a lokacinda yake ziyarar wani aikin hanyar dogo tsakanin Lagos da Ibadan, yace aikin zai taimakawa harkokin kasuwanci da tattalin arzikinn Najeriya, musamman tsakanin kudu da arewa.
Ministan yayi alkawarin cewa duk karshen wata zai ziyarci inda ake wannan aiki domin tabbatar da ganin an kammala aikin akan lokaci, zuwa shekara ta 2018.
Facebook Forum