Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Da Watanni Masu Zuwa Za a Samu Rigakafin COVID-19 - Fauci


Dr. Anthony Fauci Kwararre a Fannin Cututtuka Masu Yaduwa

Kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa na Amurka Dr Anthony Fauci, ya fada wa ‘yan majalisar dokokin Amurka cewa za a samar da rigakafin cukar coronavirus nan da ‘yan watanni masu zuwa,.

Dr. Anthony Fauci, ya fada wa ‘yan majalisar dokokin Amurka a ranar Juma’a 31 ga watan Yuli cewa ya na da kwarin gwiwa za a samar da rigakafin cukar coronavirus nan da ‘yan watanni masu zuwa, yayin da cutar ke ci gaba da bazuwa a kasar.

“Muna sa ran daga nan zuwa karshen shekara, zamu samu rigakafin da zamu iya cewa ya na aiki kuma bai da illa, abinda Fauci ya fada kenan a gaban wani kwamitin majalisar wakilai da ke bincike akan coronavirus.

Fauci ya ce a kwanan nan aka shiga mataki na karshe cikin matakai 3 na gwajin rigakafin.

A jawabin bude zaman, shugaban kwamitin na jam’iyyar Democrat James Clyburn da dan jam’iyyar Republican Steve Scalise, sun tafka muhawa akan ko gwamnatin Trump na da wata dabara ta magance annobar coronavirus ko a'a.

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG