Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na'urorin da ake zubarwa a kasashen Afrika sun fara zama matsala


Irin na'urorin computa da ake zubarwa da ake cewa E Waste da turanci.

Matsalar zubar da na'urorin injin mai kwakwalwa ko com[uta da ba'a so da ire irensu kamar wayar cellula a Afrika ta fara yin kamari.

Zubar da na'urorin da ba so irinsu computa da ire irensu a nahiyar Afrika da ace cewa E waste da turanci ta fara zama matsala. A duk shekara irin iren wadannan karikitai ton miliyan hamsin ne ake jibgewa a Afrika, kuma daga cikin wadannan adadi kasa da rubu'i guda ne ake narkarwa ake sarafa wasyu abubuwan dasu.

Yawancin irin wadannan na'urori suna shiga kasashe Afrika ne da suna taimao ko kyauta ko kuma na sayarwa. Bayan an dan yi amfani dasu, sai a zubar dasu. To amma kasar Kenya tana kokarin zama zakaran gwajin dafi a gabashin Afrika wajen kafa cibiyar da za'a narkar da irin wadannan naurori a sarafa wasu abubuwa dasu.

Dalibai makarantar Primary ta Our Lady of Nazareth a birnin Nairobin Kenya, daya daga cikin makarantun da suke amfani da na’urorin computa kwane ko second hand wadanda aka riga aka yi amfani dasu, da wasu kungiyoyin masu zaman kansu daga kasashen turai suka basu gudumawa ko kyauta. Irin na’uorin computan da aka yiwa kwaskwarima. To amma yawancin na’urorin computa da ake baiwa kasashen Afrika gudumawa ko kyautarsu ba masu daraja ne sosai bane.

Esther Mwiyeria masaniyar fasaha ce, a wata kungiyar da ake cewa Ge sci a takaice, wata kungiyar da Majalisar Dinkin Duniya ke baiwa kudin gudanar da ita wadda take taimakon kasashe masu tasowa wajen amfani da fasahohin zamani ko ICT a takaice domin inganta tsarin illimi.

Esther tace abun takaice, irin wadannan na’urorin computa da aka bada guduarwasu gudumawa, dududu moriyar da ake samu daga garesu bai wuce na tsawon shekara daya ko shekaru biyu. Tace ko a lokacin ana kashe kudi sosai wajen yin gyare gyare a saboda bini bini na’urorin ke lalacewa. Tace abun ban haushi bayan shekara daya ko shekaru biyu ana amfani dasu tilas a zubar dasu a bola da ake cewa e-waste da turanci. Gashi kuma kasashen Afrika basu da hanyoyin tinkarar irin gubar dake tattare da zubar da irin wadannan na’urorin.

Yawancin na’urorin computa kwance suna fitowa ne daga kasashen turai, a zaman na kyauta ko kuma na sayarwa.

Neelie Kroes itace mataimakiyar shugaban kungiyar kasashen turai. Neelie ta fadawa Muryar Amirka cewa kasashen turai sun zartar da tsauraran dokoki akan yadda ake zubar da na’urori da ake cewa e waste a cikin gida da kuma kasashen waje. Dokokin sun tanadi cewa tilas a narkar su ta yadda za’a sake amfani dasu wajen sarafawa wasu abubuwa ake cewa re cycling da turanci ko kuma a zubar dasu ta yadda ba zasu yiwa mutane lahani ba.

A saboda haka tace, tana ganin yana da muhimmanci kasashen Afrika suma su san yadda zasu tinkari irin na’urorin da ake zubarwa, wadanda kila su yi wa jama’a lahani ta hanyar gurbata yanayi.

Neelie tace gaskiya kam ga kasashe masu tasowa, idan basu kyautar naurorin da basu dasu, ba zasu yi la’akari da barazanar dake tattare dasu ba. A saboda haka take ganin ya kamata kasashen da suke bada taimako ko kuma gudmawar na’urori kwance su san irin matakan da su zasu dauka domin kare jama’a daga lahanin irin wadannan na’urori. Tace ya amata a fara yin la’akari da yanayi kafin daga baya ayi tunani yadda za’a zubar dasu.

Kasar Afrika ta kudu, itace kasar Afrika kawai da take da dokar data danganci irin wadannan na’urori da ake zubar. Kasar Kenya tana da ka’idodin da ake sa ran cikin shekaru biyu a fara amfani dasu. Haka kuma kasar Kenya ta fara zama zakaran gwajin dafi tsakanin kasashen gabashin Afrika a farni kafa cibiyar narkar da kayayyakin kwance da aka bata tana narkarwa tana sarafa wasu abubuwa dasu. Tun lokacinda aka kafa wannan cibya a shekara ta dubu biyu da bakwai, cibiyar tanarkar da na’urorin computa dubu hudu aka sarafa wasu abubuwa dasu da ake cewa, recycling da turanci.

XS
SM
MD
LG