Accessibility links

Ana Jana'izar Wangari Maathai A Kasar Kenya


Gungun jama'a su na bin motar dake dauke da gawar Wangari Maathai, asabar 8 Oktoba 2011 a Nairobi, Kenya.

Al'ummar Kenya su na binne macen Afirka ta farko da ta samu lambar yabon zaman lafiya ta duniya ta Nobel

Yau asabar a birnin Nairobi, al’ummar Kenya su na jana’izar macen farko ‘yar Afirka da ta taba samun lambar yabon zaman lafiya ta Nobel.

A ranar lahadi Wangari Maathai ta mutu tana da shekaru 71 da haihuwa, bayan da ta jima tana fama da cutar sankara.

Ta lashe lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya a shekarar 2004 a saboda matsayinta na kare hakkin matan kasar Kenya da kuma muhalli a kasar.

Maathai ta kafa kungiyar Green Belt Movement wadda asalinta shi ne gwagwarmayar kare marasa galihu da matalauta, musamman mata. Har ila yau kungiyar ta yi gwagwarmayar kare muhallin kasar Kenya kafin a fadada ta har ta kunshi gwagwarmaya kan batutuwan siyasa da na tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG