Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDC Ta Gudanar Da Zangar-zangar Lumana Kan Rajistar Masu Zabe A Ghana


Masu zanga zanga a Ghana
Masu zanga zanga a Ghana

 Asiedu Nketiah ya bayyana muhimmancin zanga-zangar da suke gudanarwa a duk yankuna 16 na kasar, tare da kira ga magoya baya da su jajirce wajen ganin an tabbatar da gaskiya a zaben.

Babbar jam’iyar adawa a Ghana, NDC, ta gudanar da gagarumar zanga-zangar lumana a duk fadin kasar, ranar Talata, don kalubalantar hukumar zabe (EC) ta amince a gudanar bincike kan rijistar masu kada kuri’a.

Jam’iyar NDC dai na zargin hukumar da kin ba da damar gudanar da bincike na tantance rijistar masu kada kuri’a gabanin zaben watan Disamba, bayan da ta gano cewa an tafka kura-kurai da dama a rijistar da suka hada da canzawa masu kada kuri’a runfunan zabe ba bisa ka’ida ba, a wurare daban daban, lamarin da ta ce wani yunkurin hukumar ne na yin magudi a zaben 7 ga watan Disamba 2024.

Shugaban jam'iyyar NDC, Johnson Asiedu Nketia
Shugaban jam'iyyar NDC, Johnson Asiedu Nketia

Shugaban jam’iyar adawa ta NDC, Johnson Asiedu Nketia da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyar, a shatale-talen Kwame Nkrumah da ke birnin Accra, gabanin fara tattakin. Yace: "Bukatunmu mai sauki ne, Muna son EC ta tabbatar da gudanar da zabe cikin walwala, aminci, ba tare da magudi ba, sannan kuma a samu ingantacciyar rajistar masu zabe, shi ne jigon manufarmu."

Asiedu Nketiah ya bayyana muhimmancin zanga-zangar da suke gudanarwa a duk yankuna 16 na kasar, tare da kira ga magoya baya da su jajirce wajen ganin an tabbatar da gaskiya a zaben.

Ya kara da cewa, “kowace dimokuradiyya a wani lokaci, tana fuskantar barazana. Dimokuradiyyar Ghana tana cikin babbar barazana a yanzu, kuma muna so mu yi nasara. Ba mu son komai sai zabe na gaskiya wanda zai tabbatar mana da ‘yancin zaben shugabanninmu. Ba tare da 'yancin zaben wanda muke so ba, dimokuradiyya tana kan hanyar shudewa.

Yayin zanga-zangar lumana da jam'iyyar adawa ta NDC ta shirya a Ghana
Yayin zanga-zangar lumana da jam'iyyar adawa ta NDC ta shirya a Ghana

Gabanin nan, rundunar ‘yan sandan Ghana ta sake jaddada aniyar ta na tabbatar da gudanar da zanga-zangar cikin lumana da nasara, kamar yadda darektar hulda da jama’a ta hukumar ‘yan sandan Ghana, ACP Grace Ansah-Akrofi ta yi jawabi ga manema labarai.

Ta ce: “A dukkan manyan biranenmu 16 kwamandojinmu sun dauki aniyar jagoranci; sun shirya tsaf don ganin an kammala wannan zanga-zangar cikin nasara.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki, suka bi wasu manyan titunan birnin Accra, dauke da rubuce-rubucen dake jaddada manufar zanga-zangar da suke yi, zuwa majalisar dokokin Ghana suka mika korafinsu a hukumance. Shugaban masu rinjaye Alexander Afenyo-Markin, wanda ya karbi takardar korafin a madadin kakakin majalisa, ya tabbatar wa NDC cewa majalisar za ta duba bukatunsu, kuma za a magance matsalolin ta hanyar tattaunawa.

Mahalarta zanga-zangar da NDC ta shirya a Ghana
Mahalarta zanga-zangar da NDC ta shirya a Ghana

A hukumar zabe kuma, Mataimakin kwamishinan tsare-tsare, Samuel Tettey ne ya karbi takardun korafin, a madadin shugabar hukumar zabe, Jean Mensa.

Wasu magoya bayan jam’iyar NDC da suka halarci zanga-zangar suka ce sun zo wurin zanga-zangar ne don hukumar zabe ta tabbatar da jam’iyarsu idan sun lashe zabe, sannan kuma su kalubalanci hukumar zabe dake yunkurin yin magudi a zabe mai zuwa don canja runfunar zaben jama’a domin kada su samu damar yin zabe.

Sai dai hukumar zabe ta dage a kan cewa ta yi gyaran da ya dace a rijistar masu zaben, kamar yadda mataimakin shugabar hukumar, Dokta Bossman Asare, yace a wata hira da ya yi da kafar labarai ta JoyNews kan zanga-zangar. Yace: “Mu a hukumar zabe muna ganin cewa, shugabannin NDC da suka bi hanyar gudanar da zanga-zangar suna wuce gona da iri, suna fadar ababan da babu su rajistar.

Dokta Asare ya kara da cewa, hukumar zabe ta bayyana karara ga jam’iyar NDC, da abokan hulda na kasa da kasa da al’ummar Ghana cewa rijistar tana da inganci, don hukumar ta yi duk gyare-gyaren da ya kamata. Yace, “Duk mun shirya yin zabe cikin kwanciyar hankali, kuma muna sha'awar a yi sahihin zabe”.

Ita kuma kuma jam’iyar NDC a nata bangaren ta yi zargin cewa ta gano cewa an sauyawa mutane kimanin 243,540 runfunan zabe a cikin rijistar, wanda hakan ya sa ba ta amince da hukumar zaben ba.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako daga Accra:

NDC Ta Gudanar Da Zangar-zangar Lumana Kan Rajistar Masu Zabe A Ghana.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG