Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neja: Ana Zargin Wata Matar Aure Da kashe Mijinta Amma Ta Musanta


Iyalan wani magidanci mai suna Danlami Abdullahi, da aka fi sani da suna Dan Hajiya, na zaman makomi a garin Kontogora na jihar Neja, a sakamakon rasuwar da yayi ta sanadiyyar murde masa mazakunta da ake zargin matarsa ta yi masa.

Bayanai sun nuna cewa an sami sabani ne a tsakanin marigayin da matarsa mai suna Rahanatu Abdullahi, wadda suka kwashe tsawon shekaru Takwas suna tare a matsayin miji da mata har ma da ‘ya’ya uku, lamarin ya faru ne ta sanadiyyar Karin aure da ya ce zai yi amma wadda ake zargin ta musanta.

Hajiya Kande Ahmad, mahaifiya ce ga marigayin kuma ta bayyana cewa ta iske su a sa’ilin da suke fada da juna, ta kara da cewa marigayin ya bayyana mata cewa matar tasa na rike da gabansa, kuma taki saki sai da ta yi kuwwa domin neman dauki daga jama’a.

Muhammadu Sani Usman, dake zaman dan’uman marigayin ya bayyana cewa yayin da suka je asibiti, marigayin ya bayyana masa cewa ciwon zuciya ke damunsa.

Wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari, ya sami zantawa da matar marigayin wadda ta bayyana masa cewa babu kamshin ngaskiya a cikin maganar domin a cewarta mahaifiyarsa na kokarin kare shi ne kawai.

Rundunar ‘yan sadan jihar ta bayyana cewa bata da masaniya a kan afkuwar lamarin amma ta bayyana cewa zata fara bincike kan lamarin daga yau litini.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG