Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neja: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga a Kofar Majalisar Dokoki


NEJA: 'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya

A jihar Neja, jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa daruruwan masu sana’o’in hannu da suka gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da wasu kudaden haraji da gwamnatin ke karba.

Masu zanga-zangar da suka hada da kungiyoyin masu motocin sufuri da kanikawa da masu aikin Walda da kuma masu facin Taya, sun taru gaban Majalisar Dokokin jihar Neja ne domin mika kukansu kan takurawar da suka ce ana yi musu. Amma sai jami’an tsaro suka fatattakesu da barkonon tsohuwa.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Mallam Idris Mohammad, ya ce sun dauki matakinne kasancewar gwamnati ta takura musu, kasancewar duk mambobin kungiyar kowa ya biya kudaden haraji sama Naira dubu talatin, sai gashi gwamnati ta sake turo wani kamfani domin ya karbi haraji.

Kakakin ‘yan sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana, ya ce dalilin tarwatsa masu zanga-zangar shine domin sun kashe hanya kimanin awanni biyu babu mai iya wucewa.

Shi kuma kakakin gwamnatin Neja, Mr. Jonathan Batsa, ya ce rashin biyan kudaden haraji shine dalilin kawo ‘dan kwangila domin karbar harajin. Inda yayi kira ga gamayyar kungiyoyin da su zo su zauna da gwamnati domin a tantance.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG