Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neman Belin Yahaya Bello: Kotu Ta Saka Ranar 10 Ga Watan Disamba


Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a kotu
Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a kotu

A baya an yi ta wasan buya tsakanin Bello da hukumar EFCC da ta shigar da karar shi kan zargin wawure kudaden jihar ta Kogi - zargin da ya musanta.

Babbar Kotun da ke sauraren karar da aka shigar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a Abuja kan zargin sama da fadi da kudaden jihar, ta saka ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ko za ta ba da belinsa.

Tsohon gwamnan na Kogi wanda yake tsare a ofishin EFCC a Abuja, na fuskantar tuhuma kan badakalar Naira biliyan 80 da ake zargin ya wawure na jihar a lokacin mulkinsa.

An kuma shigar da wata sabuwar tuhuma kan wawure Naira biliyan 110 – tuhume-tuhumen da duk ya musanta.

A zaman da kotun ta yi a ranar Juma’a kamar yadda kafar talabijin ta kasa NTA ta ruwaito, Mai Shari’a Maryann Anenih, ta ce a ci gaba da tsare Bello da sauran mukarrabansa da ake tuhuma har sai ranar ta 10 ga watan Dismba.

A baya an yi ta wasan buya tsakanin Bello da hukumar EFCC da ta shigar da karar shi kan wawure kudaden.

Sai a farkon makon nan ne hukumar ta EFCC ta kama Bello bayan da ya mika kansa.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG