Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Natenyahu Na Shirin Kafa Gwamnati


Benjamin Netanyahu Yace A Shirye Yake Yayi Sassauci Mai Zafi Domin Cimma Zaman Lafiya Da Falasdinawa

Firai Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce nan da makwanni biyu zai kafa gwamnati bayan nasara da ya samu ta lashe zaben da aka gudanar a ranar talatar da ta gabata.

Bayan kusan kammala kidayar kuri’un zaben, jam’iyar Mr Netanyahu ta Likud ta samu kujeru 30 wanda hakan ya dare 24 da jam’iyar hamayya ta ‘yan Zionist ta su ka samu.

Wata sanarwa da ofishin Mr Netanyahu ya fitar, ta nuna cewa yanzu haka ya soma tuntubar sauran kananan jami’yu domin hada kujeru 61 na hadakar da yake bukatar jagoranci.

Daya daga cikin Jam’iyyun it ace Kulanu wadda ta lashe kujeru 10 a zaben, kuma tuni shugaban jam’iyar ta Zionist Union, Isaac Hergoz, ya amince da cewa sun sha kayi, har ma ya taya Mr Netanyahu murna ta wayar talho.

Firai Ministan dai ya nema ne ya yi ta zarce a wa’adi na hudu idan har ya yi nasarar samun abokanan tafiya na gwamnatin hadaka.

XS
SM
MD
LG