Bayanai sun yi nuni da cewa Neymar, dan shekara 28, na jin dadin zamansa a club din saboda haka yana shirin sabunta kwantiraginsa.
A watan Yunin shekara mai zuwa kwantiraginsa zai kare wanda ya saka hannu a shekarar 2017 a lokacin da ya yi kaura daga Barcelona akan pam miliyan 200
A da, an yi ta yamadidin Neymar zai koma Barcelona a lokacin da aka dan bude kasuwar ‘yan wasa a watan Yunin 2019, amma yanzu bayanai sun yi nuni da cewa zai yi zamansa a Faransa.
A watan Disamba, shugaban kungiyar Nasser Al-Khelaifi, ya ce suna da kwarin gwiwar Neymar da Kylian Mbape za su ci gaba da zama a PSG.
A lokacin da ya yi ruwan kwallo uku a wasan karshe na gasar zakarun turai tsakanin PSG da Istanbul Basaksehir a watan Disamba, Neymar ya jaddada sha’awarsa ta ci gaba da zama a Paris.