Kungiyar ta dauki matakin ne bayan da aka yi waje da ita a gasar Europa yayin da take zaune a matsayi na 11 a gasar ta Ligue 1.
Wata sanarwa da club din ta fitar da safiyar Juma’a ta ce Vieira wanda ya fara jagorantar kungiyar ta Nice daga lokacin bazarar 2018, ya daina zama kocin kungiyar.
Dan shekara 44, Vieira ya kasance tsohon dan wasan Arsenal da ya takawa kungiyar muhimmiyar rawa kuma jigo a tawagar ‘yan wasan kasar Faransa a shekarun baya.
Jaridun wasanni na Faransa sun ruwaito cewa a daren ranar Alhamis aka sanar da Vieira wannan mataki da kungiyar ta dauka.
A halin da ake ciki kungiyar ta ayyana Adrien Ursea a matsayin kocin rikon kwarya yayin da take shirin kaiwa Reims ziyara a karshen makon nan.
Vieira ya fara jagorantar Nice ne a watan Mayun 2018 bayan da ya jagoranci kungiyar New York FC a gasar MLS ta Amurka.
Sannan ya yi aiki cikin tawagar da ke horar da ‘yan wasan Manchester City bayan da ya yi ritaya a fagen kwallo.
Cikin kakar wasanni biyu da ya kwashe a matsayin kocin Nice, Vieira ya kai kungiyar matsayi na bakwai a gasar ta Ligue 1, abin da ya ba shi damar shiga gasar Europa a kakar wasan da ta gabata.