Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Niger: Amurka na gina sansanin sojojinta mayakan sama a Agadez


Sakataren tsaron Amurka James Mattis,
Sakataren tsaron Amurka James Mattis,

Ta bakin mai magana da yawun mayakan saman Amurka a nahiyar Turai da Afirka, Amurkan na gina sansanin sojojin mayakan samanta a garin Agadez da zummar shawo kan mayakan sa kai da suke addabar yankin sahel.

Wata jami’arsojan Amurka Auburn Davis ta fadawa Muryar Amurka cewa nan da yan watanni masu zuwa Amurka za ta kamalla gina wani sansanin sojan mayakan samaa kasar Niger inda jiragen yaki da ba su da matuka za su auna kungiyoyin yan yakin sa kai da suke gudanar da harkokin su a yankin.

Mai magana da yawun mayakan saman Amurka a turai da Afrika Auburn Davis ta ce ya zuwa yanzu rundunar mayakan Amurka ta kashe dala miliyan tamani da shidda da rabi wajen gina sansanin sojan. Ta kara da cewa duka duka aikin gina sansanin zai ci kudi dala casa’in da takwas da rabi.

Ta ce wannan sansanin da ake ginawa a birnin Agadez dake arewacin jamhuriyar Niger, shine sansanin mafi girma a tarihin gine gine na rundunar mayakan saman Amurka cikin nahiyar Afirka.

Birnin Agadez ya kasance muhimmin wuri cikin hamadar sahara kuma a cikin sauki mayakan sa kai da masu fasa kauri daga Libya da Algeria da Mali da kuma kasar Chadi su na amfani dashi a zaman wurin yada zango.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG