Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIGER STATE: Shin APC Zabe Zata Yi Ko Nadi?


APC

APC ta shiga wata rigima a zaben fidda gwani saboda zaben kananan hukumomi inda ake zarginta da dauki dora

Bisa ga wasu alamu zaben fidda gwani na neman shugabancin kananan hukumomin jihar Neja a jam'iyyar APC mai mulkin jihar ya bar baya da kura.

Da dama cikin wadanda suka tsaya zaben fidda gwani sun koka akan yadda suka ce an yi masu karfa karfa.Wani Zubairu Muhammad Badamasi daya daga cikin 'yan takaran a karamar hukumar Wushishi ya yi zargin an cire sunasa daga takardar kada kuri'a duk da cewa an tura sunasa wurin SSS cewa ya cancanta ya tsaya zabe.

Zubairu yace ya je wurin SSS domin su yi masa tambayoyi daga bisani aka tura sunansa zuwa hukumar zabe ta kasa wato INEC. A shari'ance yace ya bi duk ka'idodin da aka gindiya masa. Amma ranar zaben sai aka kawo takardar zaben aka fada masa wai an cire sunansa an mayae gurbinsa da sunan wani.

A karamar hukumar Mokwa kuwa matasan yankin sun zargi mataimakin gwamnan jihar da kokarin murde masu wanda suka zaba. Suleiman Salihu Abdullahi mai magana da yawun matasan yace a zaben matasa sun samu kuri'u 74 kana dattijai suka samu 30 kawai. Ya kira mataimakin gwamnan ya barsu da sakamakon zabensu. Sun kai kokensu wurin dattawa sun kuma sa masu bakin alheri amma banda mataimakin gwamna wanda ya ki kememe.

Amma sakatariyar yada labarai ta mataimakin gwamnan Hajiya Maimuna Kolo ta karyata zargin.

A halin da ake ciki dai uwar jam'iyyar ta jihar Neja tace tana tattaunawa domin neman bakin zaren yadda za'a warware matsalolin. Injiniya Muhammad Imam shi ne shugaban jam'iyyar a jihar yace suna cikin tattaunawa domin su sasanta.

Wasu shugabannin jam'iyyar na cigaba da baiwa jama'a hakuri game da rudanin da ya dabaibaye APC. Onarebul Shehu Sulo dan majalisar wakilan Najeriya karkashin APCin daga jihar yace wasu ne suke son su cusa 'yan takaran da jama'a basa so.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG