Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Ta Nigeria Ta bada shawarar Dage Zabe Zuwa Watan Afrilu


Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ne yake daga wa taron jama'a hannu kafin kaddamarda gangamin kyamfen dinsa na neman zabe a Abuja, Nigeria.

Hukumar tace dage zaben zai bata sukunin shiryawa sosai domin kaddamar da zabe sahihi dai zai zama karbabbe.

Shugaban hukumar zaben Najeriya ya bada shawara cewa a daga zabe daga watan janairu zuwa Afrilu domin ba hukumar isasshen lokacin shirin zaben. Shugaban hukumar Attahiru Jega ya bayyana Talata cewa, hukumarsa zata gamu da cikas idan aka gudanar da zaben a watan janairu kamar yadda aka tsara.

Jega yace ya bukaci shugabannin siyasa su duba yiwuwar daga zabukan da ‘yan Najeriya zasu zabi shugaban kasa da ‘yan majalisa da kuma gwamnonin jihohi. Prof Jega ya bayyana cewa yana yiwuwa a gudanar da zabe bisa ga yadda aka tsara yanzu sai dai yin haka yana tattare da hadari.

"Duk da yake lokaci ya kure mana, bai nuna cewa ba za a iya gudanar da zaben a cikin watannin da aka tsara ba.Sai dai abinda wannan ke nufi shine babu lokacin yin wadansu sauye sauye musamman abinda ya shafi kayan aiki. Dama ana gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu ne, sai dai farkon shekarar nan ‘yan majalisa suka dawo da zaben watan janairu domin bada isasshen lokacin warware korafe korafe. Prof Jega ya bayyana cewa hukumar tana bayyanawa jama’a damuwarta ne dangane da tsarin lokacin gudanar da zaben sabili da tana son al’umma ta gamsu da aikin."

“Bashi da amfani bin tsarin da zai kai ga gudanar da zaben da ba zai zama karbabbe ba. Bisa ga tsari dai za a yi rajistar masu kada kuri’a cikin makonni biyu na farkon watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG