Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawarga Amurka da Kasashen Yammacin Duniya Sun Fice Da Zauren Majalisar Dinkin Duniya


Masu zanga zanga kan Iran a harabar Majalisar Dinkin Duniya

Saboda zargin cewa Amurka ce ta kitsa kawowa kanta harin ranar 11 ga watan Satumban 2001,wakilan Amurka da na kasashen yammacin Duniya duk suka fice daga taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Alhamis,tawagar Amurka da ta wasu kasashen yammacin Duniya,sun fice daga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya lokacin da shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad yake jawabi,bayan da yace galibin jama’a a fadin Duniya, sun yi amannar cewa gwamnatin Amurka ce ta kitsa harin 11 ga watan satumban 2001.

Mr.Ahmadinejad ya gayawa shugabannin kasashen Duniya a taron babban zauren cewa, jami’an Amurka ne kadai suka yarda cewa ‘yan ta’adda da suka sace jirage ne suka kai harin da ya rusa gine ginen cibiyar hadadar kasuwanci ta Duniya dake New York, da kuma jirgin da ya kai hari kan ma’aikatar tsaro ta pentagon.

Haka kuma shugaban na Iran ya yi magana kan barazanar kona al-Qur’ani,da wasu kungiyoyin addini suka yi, ya kira hakan “mummunar abu”.Shugaban na Iran ya rike al-Qur’ani da Bible,yana cewa mutanen Iran suna mutunta dukkan addinan biyu. Ofishin jakadancin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya nan da nan ya fitar da sanarwa,yace maimakon shugaba Ahamidinijad ya gabatar da muradun ‘yan kasar Farisa,ya gwammace gabatar da hasashe maras tushe da kuma nuna kiyayya ga yahudawa.

XS
SM
MD
LG