Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu A Afirka Ta Kudu Taki Bada Belin Tsohon madugun 'yan Tawayen Niger Delta Henry Okah


Wani sojan yan tawaye ne ke daga bindigarsa samfurin AK 47 a yayinda yake sintiri a yankin Niger Delta.

Henry Okah yana hanun hukumomin Afirka ta kudu tun bayan harin boma bomai da aka kai birnin Abuja,ranar bikin tunawa da samun 'yancin kan kasar,wanda ya halaka fiyeda mutane 10.

Kungiyar tsageran ‘yantawayen yankin Niger Delta na Nigeria na barazanar maida kaimi sosai wajen kai hare-hare ba ji, ba gani – duk kuwa da fattatakarta da rundunar sojan kasar ta soma a yanzu. A yau ne kungiyar MEND ta ke fada, a shapinta na duniyar gizo ta internet, cewa ta umurci dakarunta das u tashi tzsaye haikan, su shiga sassace karin mutane. MEND tace ko jiya Alhamis sai da ta abkawa wan rukunin iragen ruwan yaki na sojan Nigeria a Ayakoromo dake cikin jihar Delta inda har ta hallaka 10 daga sojan, da kuma raunana wasu 17.

Ta wani gefen kuma…alkalin wata kotun Afrika ta Kudu yaki yarda ta bada belin daya daga cikin jigon mutanen da ake zargi da yin hannu wajen girka bama-bamman dasuka tashi a Abuja a ranar da ake shagalin cikar shekaru 50 da samun mulkin kan Nigeria. Shi wanda aka hana belin nashi, Henry Okah, wanda ake zargin cewa tsohon shugaban kungiyar tsageran MEND ne, yana fuskatar tuhumar aiyukkan ta’addanci dake da alaka da tashin wadanan bama-bamman na Abuja da suka hallaka mutane 12. Jim kadan bayan wannan ta’addancin ne aka cafke shi Okah a can ATK, kuma ko bayanshi, hukumomin Nigeria sun kame mutane 9 da suka hada harda wani kanensa mai suna Charles, su ma duk saboda alakar da ake cewa suna da, da wa’adancan bama-bamman da suka tashi a birnin tarayya.

Har way au gameda Nigeria din dai…hukumomin Nigeria sunce sun sake kama wata kontena dake dauke da kilograma 130 na hodar heroin da ake jin ita ma daga Iran aka aiko ta. Hukumomin na Nigeria sunce sun cake akwatin ne a tashar jiragen ruwa ta lagos bayan da aka rada musu cewa akwatin na tafe tun kamnar wattanmi hudu da suka shige. Ance an cvusa hodar ne a cikin kayan gini.

XS
SM
MD
LG