Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gungun manyan siyasa daga arewacin Najeriya sun zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar,daga cikin wasu manyan masu takara da zai kara da shugaba Goodluck Jonathan.


Atiku Abubakar (File Photo)

Alhaji Atiku Abubakar ne kwamitin da Mallam Adamu Ciroma yake yi wa jagoranci ya zaba, daga cikin wasu gaggan 'yan takara daga arewacin Najeriya, da suka hada da tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida,Janar Aliyu Gusau mai ritaya,da kuma gwamnan jihar Kwara Bukola Saraki.

Gungun shugabannin ‘yan siyasar Arewacin Nigeria sun bada sanarwar fidda dan takara guda daga cikin jerin manyan ‘yan siyasar Arewa dake son yin takara a zaben fidda dan takarar da zai hadu da shugaba Goodluck Jonathan dake rike da ragamar mulkin Nigeria a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Shugabannin ‘yan siyasar Arewacin Nigeria sun bada sanarwar marawa tsohon mataimakin shugaba Atiku Abubakar baya a lokacin fidda dan takarar domin ya goga da Goodluck Jonathan.

Sauran 'yan takara da suka nemi wan nan mukami sun hada da tsohon shugaban kasa a mulkin sojan kasar, janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, janar Aliyu Gusau,da kuma gwamnan jihar Kwara mai ci Bukola Saraki.

XS
SM
MD
LG