A makon da ya gabata ne dai Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da hafsoshin sojin Najeriya, inda aka tattauna yiwuwar fara janye sojoji daga wasu yankunan kasar, domin bai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaron da ba sojoji ba damar tsare yankuna.
To sai dai kuma wannan batu na cigaba da janyo cece kuce, inda wasu ke ganin zai taimaka wajen rage zarge zargen da ake wa sojoji na wuce makadi da rawa, yayin da wasu kuma ke ganin da sauran rina a gaba.
Wasu talakawa a jihohin Adamawa da Taraba da ke cikin jihohin dake da sojoji akan manyan tituna sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro sun bayyana fargabansu kan wannan matakin, wasu kuma ke yabawa.
Mallam Muhammad Ismail, tsohon editan jaridar Leadership dake nazari kan abubuwan dake faruwa a yankin arewa maso gabas yace akwai bukatar karatun ta natsu kafin a dau matakin janyewar.
Su ma kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana nasu ra’ayoyin. Ga dai wakilin Sashin Hausa Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum