Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: An zargi shugaban kasa da yin anfani da dukiyar kasa wurin neman zabe


Shugaban Nijar Mahamoud Issoufou kuma dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya a zabe mai zuwa

Kungiyoyin fararen hula suna zargin shugaban kasar Nijar Mahamoud Issoufou da yin anfani da dukiyar kasa wurin fafutikar neman zabe lamarin da ya karya dokar kasa da ta zabe.

Kungiyoyin sun ce sun lura da yadda jam'iyyar PNDS Tarayya ta shugaban kasa mai mulkin kasar ke bin hanyoyin da suka sabawa doka a zagayen da Mahamoud Issoufou ke yi yanzu domin jan hankalin talakawa su amince masa a zaben 21 ga watan Fabrairu ya cigaba da mulki.

Shugaban daya daga cikin kungiyoyin Suraji Isa yace a fili jam'iyyar dake mulki ke anfani da kadarorin gwamnati. Yace shugaban kasa da mukarrabansa irin yadda suke anfani da kadarorin gwamnati da kudin gwamnati da jami'un tsaro na gwamnati wajen yin kemfen na siyasa. Doka ta hana yin hakan. Akwai doka ta 31 da tace alatilas duk wani mai rike da mukamin gwamnati ko dan majalisa idan.yana son ya tsaya takara to dole sai ya yi murabus.

Kungiyoyin sun yi la'akari da cewa masu fafutikar neman zabe na jam'iyyar PNDS basu yi murabus ba.

To saidai a cewar jam'iyyar PNDS tun da jimawa ta dauki matakan hana 'ya'yanta yin anfani da kadarorin gwamnati domin yakin neman zabe. Saboda haka Bubakar Sabo yace zargin bashi da tushe. Yace tun lakacin da sunan mutum ya fito cewa yana tsaywa takara ya fita gwamnati. Amma shugaban kasa shugaban kasa ne har zuwa ranar da aka rantsar da sabon shugaba. Domin ya sake tsayawa zabe ba za'a hanashi anfani da dakarun tsaron lafiyarsa ba. Yakamata 'yan adawa su yi la'akari da wannan.

To saidai wani abu mai tada hankali a kasar yanzu shi ne yadda magoya bayan 'yan takara ke cirewa juna hotunan tallatar da kansu da suka manna a bainar jama'a da tutocinsu. Haka ma dabi'ar tare wani dan takara a ce ba zai wuce ba. Wadannan lamura na tada hankali kuma suna iya sa kasar cikin rikici.

'Yan siyasa sun soma shiga matasa amma ana fatan ba zasu zama 'yan bangan siyasa ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG