Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR:Bincike Na Nuna Cewa Rikicin Boko Haram Na Karuwa


Kungiyar Alternative Nijar
Kungiyar Alternative Nijar

Sakamakon bincike da wata kungiya mai zaman kanta ta fitar na nuni da cewa, ana kara samun fuskantar tashin hankali sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram

A jamhuriyar Nijar kungiyar Alternative ta fitar da rahoto a game da halin da jama’a ke ciki a yankin Diffa, sanadiyar rikicin Boko Haram, inda rayukan mutane ke salwanta yayinda satar mutane ke karuwa, duk da irin matakan da hukumomi ke cewa suna dauka.

Makwanni sama da 3 kungiyar AEC ta shafe, tana gudanar da bincike domin tantance zahirin halin da al’umma ke ciki a jihar Diffa, yankin dake fama da rikicin Boko Haram.

Karancin tallafi daga kungiyoyin agaji ya sa jama’ar da Boko Haram ta tilastawa tserewa daga matsugunansu, suka soma rungumar wasu ayyukan dake barazana ga mahalli.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG