Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR:Biyan Iyalan Ba’are Diyya Ya Dace


Tambarin Jamhuriyar Nijar

Wadansu ‘yan Jamhuriyar Nijar sun bayyana goyon bayan hukumcin da kotun kungiyar tattalin hadin kan kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yanke inda ta bukaci a biya iyalan marigayi tsohon shugaban kasar Nijar Ba’are Mai Nasara diyyar saifa miliyan dari hudu da hamsin.

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Yousef Abdoulaye, shugaban kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar, Surajo Isa ya bayyana cewa, hukumcin da cewa babban ci gaba ne. yace sun gamsu matuka, kasancewa wannan ne farkon inda gaskiya zata bayyana, sai dai ya bayyana takaicin ganin kotun bata gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka yi mashi kisan gilla ba, domin ba iyalan marigayi tsohon shugaban kasar damar yin zabi ko su gafarta masu ko kuma su nemi a hukumta su.

An kuma shawarci iyalan marigayi tsohon shugaban kasar su rungumi kaddara kasancewa, Allah ne mai sakayya, kuma rai da rayuwa suna hannunsa.

Wadansu da wakilin namu ya yi hira da su sun bayyana cewa, muhimmin abinda ya sa iyalan marigayi shugaba Ba’are suka garzaya kotu shine domin neman a gano wanda ya kashe shi a kuma tuhumeshi ba batun diyya ba.

Ga ra’ayoyin ‘yan Nijar game da hukumcin kotun

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG