Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Jam'iyar CDS Rahama Ta Kori Wadansu Kusoshinta


Hoton Abdou Labo lokacin yana takarar shugaban kasa
Hoton Abdou Labo lokacin yana takarar shugaban kasa

Jam’iyar CDS Rahama ta bada sanarwar korar wasu makarrabanta wadanda tace suna yin zagon kasa da nufin haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yayanta sai dai wadanda matakin ya shafa sun ce ba za ta sabu ba.

Taron shuwagabanin rassa da na uwar jam’iya da ya gudana a karshen mako a Yamai ne ya yanke shawarar korar jiga jigan CDS RAHAMA cikinsu har da tsohon shugabanta Abdou Labo saboda zarginsu da kokarin haddasa rudani a tsakanin ‘yayan jam’iyar tun bayan da kotu ta bayyanashi a matsayin wanda doka ta haramtawa jagorancin harkokin jama’a.

Haka kuma shuwagabanin CDS Rahama sun bada sanarwar mayarda Moutari Kadri akan mukaminsa na mataimakin shugaban reshen Zinder yayinda suka damka ragamar shugabancin jam’iya a hannun Me Madougou Boubakar.

Da yake maida martani Dr Ibrahim Halilou wanda a kawanakin baya bangaren Abdou Labo ya nada a matsayin shugaban CDS Rahama na wucin gadi ya yi watsi da wannan mataki na korarsu daga jam’iya.

Jam’iyar wace a karkashinta Mahaman Usman ya shugabanci kasar Nijar a zamanin jamhuriya ta uku, ta yi fama da rikicin shugabanci inda aka shafe shekaru kusan hudu ana tafka shara’a tsakanin bangaren Abdou Labo da na Mahamman Usman kafin a karshe a bayyana Labo a matsayin wanda yafi cancantar ya jagoranci jam’iyar.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma

Rikicin cikin gida a jam'iyar CDS Rahama-3:17"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG