Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Wasu Kafafen Yada Labarai A Jamhuriyar Nijar


Shugaban kasar Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Mahamadou Issoufou

Hukumar tace labarai a Nijar CSC ta maida martani bayan da kungiyoyin ‘yan jarida suka zargeta ta nuna halin ko in kula akan matakin rufe wasu kafafe masu zaman kansu da ma’aikatar haraji ta kaddamar a ‘yan kwanakin nan saboda rashin biyan haraji.

Binciken da ma’aikatar haraji ta gudanar a kafafe masu zaman kansu ne ya gano cewa galibi daga cikinsu ba sa mutunta tsarin haraji a tsawon shekaru da dama lamarin da ya sa aka ci kowace tasha miliyoyin cfa a matsayin tarar da ya kamata su biya kafin shudewar wani wa’adin ma’aikatar ta haraji. To sai dai kungiyoyin ‘yan jarida irinsu ‘Synatic’ a ta bakin SGA Moudi Moussa, ba su ji dadin faruwar wannan ala’amari ba, domin a cewarsa sakacin hukumar CSC ne ya haddasa shi.

Duba da yadda kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida suka yi mata ca ya sa hukumar ta CSC fitar da wata sanarwar da aka rarrabawa manema labarai domin kare kanta daga zargin kwance da kaya.

Hukumar ta CSC a wannan sanarwa da shugabanta Kabiru Sani ya sanyawa hannu, ta ce akwai alamun jahilci a tare da irin wannan zargi domin aikin zuba ido daban na karbar diyyar kasa daban, saboda haka ba za ta yi katsalandan akan aikin da ya rataya a wuyan ma’aikatar haraji ba.

Da yake bayyana matsayinsa akan wannan takaddama, editan jaridar LE TEMPS Zabeirou Souley, ya ce hukumar haraji ta shaida wa wadannan kafafen da basu biya kudin da ake binsu kafin ta dauki matakin rufewa, inda wasu suka je suka yi yarjejeniya kan amince musu su biya kadan-kadan har sai sun cika kudade. Su wadannan ba a rufe su ba.

Sai dai ya kara da cewa idan an bi ta barawo yana da kyau a bi ta ma bi sahu. Ya ce da kamfanonin jarida da dama na bin gwamnati kudade amma ba ta biya ba har yanzu saboda kamata yayi a zauna a gano yadda za a warware matsalar.

Daga tsakiyar watan yuli kawo yau gidajen television masu zamn kansu 5 da jaridu 3 ne ma’aikatar haraji DGI ta rufe saboda abinda ta kira rashin cika alakwalin dake tsakaninta da su.

Saurari cikakken rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG