Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Jam’iyyar MPN Ta Zargi Gwamnati Da Kawo Tsarin Zaben Da Zai Haddasa Rudani


Hukumar Zaben Nijar wadda Ibrahim Yacuba ya ce 'yan jam'iyya daya tilo suke ciki

Bayan makwanni uku da ficewarsa tare da jam’iyyarsa ta MPN Kishin Kasa wadda yake shugabanta a gwamnatin Jamhuriyar Nijar, Alhaji Ibrahim Yacouba, ya soma zagayawa cikin kasar yana bayyanawa magoya bayansa dalilin ficewarsa daga gwamnatin hadakar.

A Birnin Konni Alhaji Yacouba ya ce sun fice daga gwamnatin kasar ta gamayyar jam’iyyu, sun shiga adawa da gwamnatin.

Ya ce sun dauki shekara guda suna jan kunnen gwamnati akan kada ta kawo wani tsarin da zai cuci kasar.

Ya kara da cewa, gwamnati ta na son ta kawo wasu ka’idojin zabe da ba’a taba yin anfani da su ba, kuma za su kawo rudani a duk fadin kasar.

Yacouba ya ce jam’yyun Nijar su ne suka zauna suka yi shawarar fito da tsarin zabe, ba jam’iyya daya tilo ba yana mai cewa tsarin da suka gada shekara da shekaru yanzu an canza shi da wani daban.

Ya ce dalili kenan da suka rubuta wasika akan sauyin da ake kokarin kawowa wanda ya ce ba shi da wani amfani ga al’ummar Nijar.

A cewarsa hukumar zaben kasar ta yanzu ta zama mallakar jam’iyya guda, jam’iyyar PNDS Tarayya dake mulki.

Sai dai kalamun na Alhaji Ibrahim Yacouba ba su yi wa jam’iyyar da ke mulki, PNDS dadi ba inda Alhaji Umaru Dan Maisaje na majalisar dokokin kasar ya ce su ‘yan Nijar suna da hankalinsu saboda sun yi shekaru 27 suna siyasa.

Ya ce duk wanda ya shiga gwamnati da wata manufa amma bai ci nasara ba, sai ya fito yana wasu maganganun marasa dadi.

Saurari cikakken rahoton Haruna Mamane Bako domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG