Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dokokin Kasa Ya Ziyarci Yankin Diffa


Jami'an Tsaron Jamhuriyar Nijar
Jami'an Tsaron Jamhuriyar Nijar

Wata tawagar kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasa ta kai ziyara a Diffa inda suka tantauna da al’umma akan halin tabarbarewar tsaron da ake ciki a ‘yan watanin nan biyo bayan hare haren da kungiyar Boko Haram ta zazafa kaiwa fararen hula da sojoji.

Ziyarar wacce ke cikin sababbin jerin ayyukan da majalisar dokokin kasa ta kudirtawa kanta a baya bayan nan, ta kasance wata damar tuntubar rukunonin al’ummar Diffa domin tantance zahirin dalilan da ke maida hannun agogo baya a yakin da dakarun Nijar ke kwafsawa da kungiyar Boko Haram yau shekaru sama da 4.

A karshen wannan rangadin tawakar karkashin jagorancin Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasa Hon. Hama Assa, ta gano abubuwa da dama ta kuma gargadi al’umma akan wasu mahimman batutuwa.

Sai dai a yayin wannan ganawa wani mai magana da yawun al’ummar yankin Diffa ya gabatar da wani sakon da suke bukatar a isar da shi zuwa ga shugaban kasa Mahamadou Issouhou.

A nan gaba kadan majalisar dokokin kasa za ta gudanar da mahawarar bainar jama’a akan abubuwan da rahoton tawwagar kwamitin tsaron ya gano a yayin wannan ziyara da nufin tantance shawarwarin da zasu taimakawa gwamnati wajen shayo kan matsalar tsaron da ke ci gaba da lakume rayukan al’umma tare da haddasa asarar dimbin dukiyoyi da kaurar jama’a.

Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma

Kwamitin tsaro ya kai ziyara Diffa-2:59"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG