Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Na Fuskantar Barazanar 'Yan Ta'adda Masu Alaka Da Kungiyar IS


Shugaba Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou

Wani babban jami’in tsaro a Jamhuriyar Niger ya fadawa Muryar Amurka cewa, ayyukan da kungiyoyin tsageru da dama ke gudanarwa a kan iyakokin kasar, na barazana ga harkokin tsaro a Nijar da baki dayan yankin.

Ministan Tsaro Kalla Mountari ya fadawa Muryar Amurka cewa kungiyoyin tsagerun wadanda ke da alaka da kungiyoyin IS da Al Qaeda, na da babban hadari ga kasar, za kuma su iya kutsa kai cikin kasar idan har mahukuntan yankin ba su dauki tsauraran matakan kariya ba.


Ya kara da cewa, barazanar kungiyoyin ka iya shafar tsaron nahiyar turai, idan har suka samu damar kafa tunga a kasar ta Nijar, idan aka yi la’akkari da kusancin kasar da Libya, lura kuma da yadda Libyan ba ta da tsayayyar gwamnatin da za ta iya dakile tsagerun daga tsallakawa zuwa nahiyar turai.


Wannan gargadin da ya fito daga bakin babban jami’in tsaron kasar ta Nijar dangane da tsagerun, ya biyo bayan wani rahoto da ya nuna cewa Amurka ta fara kintsa jiragenta mara- matuka, a wani yunkuri da take yi na tattara bayanan sirri domin gano mabuyar kungiyoyin tsagerun a yankin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG