Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Na Shirin Karbe Mitocin Kafofin Yada Labaran Da Ba a Amfani Da Su


Wasu daga cikin shugabannin gidajen talbijan da radiyo masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, manajojin tashoshin rediyo da na talbijin masu zaman kansu, sun fara nuna damuwa akan wani abinda suka kira shirin rufe tashoshinsu bayan da hukumar sadarwa ta soma duba hanyoyin karbe mitocin watsa shirye-shiryensu kan cewa sun saba yarjejeniyar da ke tsakaninta da su.

Wani bincike da hukumar CSA ta gudanar, ya gano cewa wasu tashoshin FM da gidajen talbijin masu zaman kansu ba sa amfani da miticon da aka ba su domin soma aikin yada labarai.

Hakan ya sa hukumar da ke ba da lasisin fara watsa shirye-shirye ta kudiri aniyar karbe mitocin.

“Akwai wandanda tun da aka ba su mita da lasisi ba su taba aiki ba sam, yau shekara hudu, biyar shida ba su taba aiki ba, wadansu kuma sun fara aiki suka tsayar da aikin, amma ba su maido da wadannan mitocin ba.” A cewar shugaban hukumar ba da lasisi ta CSA, Abdurrahman Usman.

Sai dai kungiyar manjojin radiyo da talbijin masu zaman kansu sun nuna mamakinsu kan wannan mataki da hukumar ta CSA ke shirin dauka.

“Sun sani cewa ba kowa ba ne yake da dama a jihar da aka bashi izini ya bude gidan talbijin ya kuma bude na radiyo. Wasu ma sun rubuta masu cewa matsala ce suka samu ta kayan aiki da suka lalace kuma suna kan gyara idan aka kammala za a ci gaba da aiki.” In ji kakakin kungiyar manajojin, Lamin Suleiman.

Saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Yadda Aka Yi Na Samu Mabiya Miliyan Daya a Shafina Na Instagram - Daso
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG