Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Tare Masu Neman Zamowa Bakin Haure A Cikin Hamada


Hoton daya daga cikin motocin a-kori-kura da suka lalace har mutane 92 suka mutu a cikin hamadar arewacin Nijar.
Hoton daya daga cikin motocin a-kori-kura da suka lalace har mutane 92 suka mutu a cikin hamadar arewacin Nijar.

Hukumomin sun tare mutane 127 dake kokarin zuwa kasar Aljeriya bayan da suka bar Arlit cikin wasu motoci 5

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tare wasu mutane 127 dake kokarein tsallaka hamada zuwa cikin kasar Aljeriya, kwanaki kadan a bayan da aka tsinci gawarwakin mutane 92 bakin haure da suka yi irin wannan kokarin tsallakawa zuwa can.

Jami’ai suka ce an kama wadannan mutane masu niyyar zamowa bakin haure yau asabar cikin wasu motoci biyar a lokacin da suka bar garin Arlit na arewacin kasar.

Shugaban wata kungiya mai zaman kanta a Arlit yace hukumomi sun saki mutanen da ‘yan garin Arlit ne a cikin wannan tawaga.

A cikin wata hirar da yayi da Muryar Amurka, Moustapha Alhacen yace sauran mutanen da suka fito daga wasu garuruwa a cikin jamhuriyar Nijar an tasa keyarsu zuwa garuruwansu. Yace wasu kuma daga Najeriya makwabciyar Nijar suke, kuma hukumomi su na shirya yadda zasu mayarda su gidajensu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace akasarin mutanen mazaje ne, amma kuma akwai yara a cikinsu.

Jamhuriyar Nijar tana tsakiyar hanyar da baki ke bi daga kasashen kudu da hamadar Sahara zuwa Turai.

Wannan ala’amarin yana faruwa ne ‘yan kwanaki kadan a bayan da hukumomi suka gano gawarwakin da suka fara rubewa na wasu bakin haure su 92 wadanda kishin ruwa ya kashe su a lokacin da suka yi kokarin ketare hamadar Sahara. Akasarinsu mata ne da yara kanana.
XS
SM
MD
LG