Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Takaddama Ta Barke Tsakanin PNDS, Moden


Wani matashi dan kasar Falasdinu nayin wani rikici
Wani matashi dan kasar Falasdinu nayin wani rikici

A Jamhuriyar Nijar wata sabuwar takaddama ta kunno kai bayan da wasu magoya bayan jam’iyyar PNDS mai mulki suka zargi jam’iyyar adawa ta Moden Lumana da hannu a zanga zangar matasa da aka yi fama da ita a ‘yan kwanakin nan a birnin Yamai.

Zanga zangar ta wakana ne sakamakon kosawa da dokar hana fita da hana halartar wuraren ibada da nufin dakile yaduwar cutar COVID- 19.

Tun a farkon makon jiya ne matasa suka fara bijirewa dokar hana fita da hukumomi suka kafa daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe inda suka yi ta kona tayoyi a manyan titunan birnin Yamai.

A wasu unguwanni kuma mutane sun kosa da a dage dokar hana sallar Juma’a, abin da wasu magoya bayan jam’iyya mai mulki ke kallonsa a matsayin wani sabon salon na ‘yan hamayya.

Kakakin jam’iyyar ta PNDS, Assoumana Mahamadou ya sheda wa Muryar Amurka cewa, a ganinsa lamarin ya kasance siyasa ne kawai.

“Kai wa layin dan gidan dan jam’iyyar mu hari, ya nuna mana cewa harkar siyasa ce kawai.” Mahamadou ya ce.

Da take maida martani akan wannan zargi, uwar jam’iyyar Moden Lumana ta ‘yan adawa, ta nisantar da kanta daga zanga zangar ta matasa.

“Mutane suna zargin mu cewa muna da hannu a wannan lamarin, amma mutane suna manta cewa ba a Yamai aka fara wannan rikicin ba,” a cewar babban jigo a jam’iyyar, Ibrahim Kaza.

Domin wanke kanta daga abin da ta kira kazafi, jam’iyyar Moden Lumana ta fara yunkurin shigar da kara a gaban kotu .

‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kokarinsu na murkushe wannan tarzoma abin da ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali a unguwannin da aka yi artabu tsakanin jami’an tsaro da matasa.

A sanarwar da sashen yada labarai na hukumar ‘yan sanda ya fitar, an bayyana cewa mutum 108 ne aka kama sanadiyyar wannan zanga-zanga.

Nan take dai aka tisa keyar 10 daga cikinsu zuwa gidan yarin Koutoukale.

Saurari wannan rahoton a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG