Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Wata Kotu Ta Sallami Daliban da Aka Tsare Saboda Mummunar Zanga-zanga


Mr.Morou Amadou, ministan shari'ar kasar Nijar

Wata kotu a Yamai ta sako daliban jami'a da aka daure a gidan kaso sanadiyar zanga-zangar da suka yi na neman gwamnati ta kara dakunan karatu da malamai da dai wasu kayan da zasu taimakawa karatunsu

Wata kotun birnin Yamai ta bayyana hukuncin da ta yanke a dangane da shara’ar da ta yiwa wasu dalibai kimanin 31 da aka garkame a gidan yari biyo bayan wata mumunar zanga-zangarkungiyar dalibai taranar 19 ga watan Oktoban da ya gabata wace tayi sanadiyar konekonen motoci da fashe-fashen madubai a titunan birnin Yamai .

Sakamakon binciken da kotu ta gudanar bayan sauraren wadanan dalibai da ma’ikantan birnin Yamai suka zarga da laifin tada zaune tsaye da haddasawa jama’ar da ba su ji ba su gani ba asarar dukiyoyinsu a yayin zanga zangar da kungiyar USN ta dalibai ta shirya da nufin neman a magance masu matsalolin da suka hada da rashin wadatattun dakunan karatu da bencina da karancin malamai. Alkalin ya dauki matakin sallamar dalibai 27 daga cikin 31 da suka shafe makwanni 3 a gidan kaso yayin da sauran 4 suka samu sakin talala to sai dai wannan mataki ya zamewakungiyar dalibai ta USN abinda bahaushe ke cewa ga koshi ga kwanan yunwa inji shugabanta USAINI SAMBO USMAN .

Su ma iyayen daliban da kotu ta sallama sun yi farin ciki da wannan mataki ganin yadda ya kawo karshen kai da kawon da suka yi fama da shi tsakanin gida da mashara’anta zuwa gidan yari a tsawon Kwanaki fiye da 20.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG