Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: 'Yan Adawa Na Zargin Jam'iya Mai Mulki Da Fara Yakin Neman Zabe


Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Rangadin da dan takarar jam’iyar PNDS Tarayya, Bazoum Mohamed ya gudanar a wasu yankunan kasar, ya janyo wasu daga bangaren ‘yan adawa wadanda ke zargin jam’iyar mai mulki, da soma yakin zabe.

Wannan shine zagaye mafi girma da shugaban jam’iyar PNDS Tarayya ke gudanarwa a yankunan karkara, tun tsayar da shi a matsayin dan takarar 2021 a watan Maris da ya gabata. Bayan yankunan Dosso da Tahoua, tawagar ta Bazoum Mohamed ta ziyarci yankin Zinder.

La’akari da faruwar wasu abubuwa a yayin jerin gangamin da jam’iyar mai mulki ta gudanar, ya sa ‘yan adawa zargin an taka doka.

Sai dai Bazoum Mohamed yace akwai rashin fahimtar nauyin da ya rataya a wuya, domin fatan samun karbuwa a wurin talakkawa..

Hotunan da aka yada a shafikan sada zumunta, sun nuna cewa dan takarar na PNDS Tarayya ya yi amfani da motarsa ta Ministan cikin gida, a yayin wannan zagaye, to amma a cewarsa, ya san cewa anan ya aikata ba dai dai ba.

Ana su bangare ‘yan adawa na ganin ya kamata doka ta yi aikinta don kawo karshen aikata irin wannan mummunar dabi’a ta ‘yan siyasa anan gaba.

Tsarin jadawalin da hukumar zabe ta fitar a karshen makon jiya na cewa a ranar 27 ga watan Disamba 2020 ne za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG