Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Za A Biya Diyyar Matasan Da Dakarun Faransa Suka Kashe A Bara


Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

A ranar 27 ga watan Nuwambar bara ne matasa suka datse mashigar garin Tera a wani lokacin da ayarin motocin sojan Barkhane ke shirin ratsa garin akan hanyarsu ta zuwa garin Gao, lamarin da ya sa Faransawan bude wuta akan wadanan mutane.

Gwamnatin Jmhuriyar Nijer ta ba da sanarwar cimma daidaito da kasar Faransa domin biyan diyya ga iyalan mutanen da suka hallaka bayan da dakarun rundunar Barkhane suka bude wuta akan masu zanga-zangar hana ayarin motocin sojan Faransa ratsa garin Tera a ranar 27 ga Watan Nuwambar bara akan hanyarsu ta zuwa garin Gao na kasar Mali.

Sai dai 'yan Nijar na cewa biyan diyya ba zai maye gurbin shara'a ba don haka dole a dauki matakin hukunta wadanda suka aikata wannan kisa.

La’akkari da yadda binciken da jami’an jandarman Nijar suka gudanar da wanda Faransa ta ce ta gudanar suka gaza gano zahirin abubuwan da suka wakana a yayin tarzomar da ta barke a garin Tera na jihar Tilabery a ranar asabar 27 ga watan November 2021, ya sa gwamnatocin kasashen biyu biyan diyya ga wadanda abin ya rutsa da su kamar yadda aka bayyana a sanarwar da gwamnatin Nijer ta fitar.

Tuni dai jami’an fafitika suka yi wa wannan batu ca, jigo a gamayyar kungiyoyin FSCN Abdou Elhadji Idi na cewa matsalar kisan matasan Tera magana ce da ta shafi tsaida doka ba wai batun biyan kudi ba.

Shi ma shugaban kungiyar Tournons La Page Maikol Zody na ganin rashin dacewar biyan diyya a maimakon maida hankali wajen daukan matakan hukunta Faransawa da suka yi wannan aika aika saboda haka yace da sake.

A ranar 27 ga watan November da ya gabata ne matasa suka datse mashigar garin Tera a wani lokacin da ayarin motocin sojan Barkhane ke shirin ratsa garin akan hanyarsu ta zuwa garin Gao lamarin da ya sa Faransawan bude wuta akan wadanan mutane inda a take 3 daga cikinsu suka rasu yayin da mutun 17 suka ji rauni.

Goma daga cikinsu sun shiga cikin mawuyacin hali abin da ya sa hukumomin kasashen biyu kaddamar da bincike wanda kuma daga bisani aka ce ba su ba da damar gano gaskiyar lamarin, mafari kenan gwamnatocin kasashen biyu suka cimma daidaito da shugabanin al’umar Tera akan maganar biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su koda yake ba a bayyana adadin kudaden da aka biya ba.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

Nijar: Za A Biya Diyyar Matasan Da Dakarun Faransa Suka Kashe A Bara - 3'12"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG