Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Za Ta Fara Warewa Fannin Ilimi Kashi 22 Cikin Kasafin Kudin Kasar


Taron Inganta Ilmi A Jamhuriyar Nijar

A wani taron da ya hada masu ruwa da tsaki a fannin ilimi shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya gabatar da manufofinsa a fannin ilimi da nufin  tattara shawarwarin da za su taimaka a magance tarin matsalolin sha’anin karatu a kasar na shekara da shekaru.

Karancin kwararrun malamai da rashin ingantatun dakunan karatu da nisan makaranta a galibin yankunan karkara da rashin tsayayyen tsarin fasalin karantarwa da kuma rashin zuba ido akan ayyukan makarantu masu zaman kansu, na daga cikin mahimman matsalolin da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bukaci mahalarta wannan taro su yi nazari akansu don samar da mafita.

Taron Inganta Ilmi A Jamhuriyar Nijar
Taron Inganta Ilmi A Jamhuriyar Nijar

Sauran sun hada da tarnakin da matsalar tsaro ke yi wa sha’nin ilimi a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Bazoum ya ce zai kebe kashi 22 daga cikin 100 na kasafin kudaden kasa domin fannin ilimi daga shekarar 2022.

Da yake bayani a madadin shugabannin kungiyoyin malaman makarantu, sakataren kungiyar malamai ta SNEN Issouhou Arzika ya ce Mohamed Bazoum ya sosa masu inda yake masu kaikayi saboda haka sun yi na’am da manufofinsa na farfadoda harkar ilimi.

Taron Inganta Ilmi A Jamhuriyar Nijar
Taron Inganta Ilmi A Jamhuriyar Nijar

Koma bayan ilimin ‘yaya mata a Nijar ita ma wata matsala ce ta daban da ke hana ruwa gudu a kokarin ilmantar da al’ummar wannan kasa saboda haka shugaban kasa ya bayyana shirin kaddamar da wani tsarin baiwa ‘yan mata damar samun ilimi mai dorewa.

Matsalar tsaron da ta addabi jama’a a yankuna na wannan kasa ta yi sanadin rufe makarantu masu tarin yawa to amma shugaba Mohamed Bazoum ya ce ya zo da wani tsarin tattara daliban irin wadannan makarantu a cibiyoyin musamman da yake shirin kafawa domin ba su damar ci gaba da karatu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


Dubi ra’ayoyi

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG