Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer: An Kafa Kwamitin Wayar Da Kan Al'umma Akan Cutar Coronavirus


A yayin da adadin masu cutar coronavirus ke karuwa fiye da kima a Jamhuriyar Nijer hukumomin kasar sun fara daukar matakan karfafa hanyoyin sadarwa da nufin wayar da kan al’uma a game da hanyoyin kare kai daga wannan annoba da tuni ta hallaka mutane 5 a kasar.

Lura da yadda wasu ‘yan Nijer ke ci gaba da bijire wa matakan dakile yaduwar cutar COVID-19, wasu kuma basu yarda da cewa wannan cutar gasikiya ce ba, hakan ya sa gwamnatin kasar kafa wani kwamiti na musamman mai kula da sha’anin sadarwa wanda kuma zai maida hankali akan ayyukan fadakarwa, a cewar kakakin gwamnatin Nijer, Abdourahaman Zakaria a lokacin wani taron manema labarai.

Kwamitin ya yi amannar cewa kafafen yada labarai musamman na kasa-da-kasa masu gabatar da shirye-shirye da harshen hausa na da rawar takawa wajen canza wa jama’a tunani a dangane da wannan mummunar cuta da ta addabi duniya. Dan jarida, bugo da kari magatakardan Ministan watsa labaran Nijer, Abdoulaye Coulibaly, shine mataimakin shugaban wannan kwamiti.

Kwayar Cutar Coronavirus
Kwayar Cutar Coronavirus

Ma’aikatar kiwon lafiyar Nijer, a sanarwar da ta bayar a yammacin jiya Laraba, ta ce a wunin jiya kawai an gano karin wasu mutane 40 da suka kamu da cutar coronavirus a Nijer, abinda ke nufin kawo yanzu mutane 74 ne suka harbu a fadin kasar, mutane 2 a jihar Maradi sauran a birnin Yamai kuma tuni 5 daga cikinsu suka rasu sakamakon wannan annoba.

Saurari karin bayani cikin sauti daga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG