Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer Ta Bayyana Yakin Russia A Ukraine A Matsayin Barazana Ga Kasashe Masu Karamin Karfi


NIGER: Ministan Kudi Hassoumi Massaoudou
NIGER: Ministan Kudi Hassoumi Massaoudou

Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun yi Allah wadai da yadda Russia ta yi fatali da dokokin kasa da kasa ta hanyar mamayar da ta yi wa kasar Ukraine.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijer Hassoumi Massaoudou dake bayyana matsayin gwamnatin kasar dangane da yakin Russia ke kwafsawa da Ukraine ya nuna a fili karara rashin dacewar wannan yaki da ke zubar da kimar nahiyar turai a game da maganar mutunta ‘yancin kasa da kasa.

Yace "tun bayan kammala yakin duniya na 2 an yi zaton ba za a sake fuskantar barkewar yaki a turai ba amma kuma yau an wayi gari nahiyar ta fada cikin yanayin yaki wanda shine mafi muni a tarihin duniya ganin yadda daga cikin manyan kasashen duniya ta mamaye makwafciyarta, abinda mu ke ganin ya sabawa dokokin kasa da kasa ya kuma sabawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya, dokokin kasa da kasa ne ke bai wa kananan kasashe irin namu damar cin gashin kansu domin ba mu da karfi idan haka siddan za a wayi gari saboda ji da kai wata kasa ta mamaye makwafciyarta ba maganar ‘yanci ko kuma dokokin kasa da kasa shi ya sa muke bin sahun kasashen dake Allah wadai da wannan mamaya irin ta zamanin Jahiliya. Hakan ne ma ya sa tun a tashin farko muka goyi bayan kudirin MDD a game da rashin cancantar wannan yaki."

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta yaba da matsayin na hukumomin Nijer dangane da yakin na Russia a Ukraine.

Tace tsarin tafiyar siyasar duniya ya shiga cikin halin kangin da bai taba fuskanta a sakamakon yakin da Russia ta kaddamar a Ukraine ba. Matsayin na Nijer abu ne dake dai dai da matsayin kasashen duniya saboda abu ne da ke taba ‘yancin rayuwa kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shata. Mu ma muna tur da kashe kashen da Rusha ke da alhakinsa a yakin da ta kaddamar.

Wadanan ministoci sun bayyana matsayin kasashen nasu ne a yayin ziyarar da minstar harakokin wajen Faransa da abokin aikinta na tsaro suka gudanar ranar alhamis da laraba a Nijer bayan tantaunawar da suka yi da takwarorinsu a game da tsarin daftarin da darakun kasashen 2 zasu yi amfani da shi a fagen daga bayan kaurar sojojin Barkhane daga Mali zuwa Nijer.

Bisa ga cewarsu alama ce dake nunin girman barazanar da kasashe masu karamin karfi ke fuskanta daga wadanda ke da ra’ayin amfani da karfin soja don cimma gurinsu akan abokin zama yau shekaru da dama bayan yakin dubiya na 2.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00
XS
SM
MD
LG