Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer Ta Soke Yafewa Kamfanonin Sadarwa Harajin 2018


Shugaban Nijer Mahamadou Isoufou

Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta kudiri aniyar fara karbar wani harajin da ta yafewa kamfanonin wayar sadarwa a shekarar 2018 bayan da ta ce ta gano wadannan kamfanoni suna da rashin cika alkawari akan maganar sayen kayan aikin samarda ingartacciyar wayar sadarwa a kasar.

Harajin da ake kira TATTIE wanne a shekarar 2017 gwamnatin ta Nijer ta yanke shawarar sasautar dashi daga tamma 88 na sefa, cfa, zuwa tamma 50 a kowane minti guda na kiran da ya shigo daga ketare.

Wannan matakin na da zummar baiwa kamfanonin selula hanyar samun kudaden shiga da zasu taimaka masu sayen kayan aiki domin inganta wannan fannin. Sai dai watanni 12 bayan hakan gwamnatin ta Nijer ta ce ta sake shawararta bisa wasu dalilai dake da nasaba da aikata rashin gaskiya a bangaren kamfanonin.

Dan majlisar dokokin kasa na bangaren masu rinjaye Boukar Sani Zilly ya yaba da wannan matakin na gwamnati. Ya ce kamfanonin sun je wajen gwamnati sun ce za su ba matasan Nijer aiki idan an rage masu haraji. Amma an gano rufa rufa suka yi kuma dole ne a kwato hakkin kasa daga garesu.

Dama dai kungiyoyinfarar hula na CCAC sun sha ganarda gwamnatin Nijer rashin dacewar wannan mataki tun fil azal har ma suka sha zanga zanga akai sai dai kiransu bai samu shiga ba a wancan lokaci, abinda Nouhou Mahamadou Arzika na MPCR ya ce gaskiya ce ta yi halinta. Ya ce an wayi gari yau gwamnati da kanta ta ga gaskiyar maganar da suka fada. Yanzu ta yi amai ta lashe amma har yanzu ba’a fada masu ba hukumcin da za’a yiwa wadanda suka rudar da gwamnati can baya akan lamarin saboda kasa ta yi asarar miliyoyin kudi.

Mutane kusan miliyan 8 daga cikin miliayn 20 na yawan al’umar Nijer ke amfani da wayar tafi da gidanka wadanda alamu ke nunin hukumomi sun yi buris da halin da suke ciki a can baya to amma da yake sun gane yau dole su canza ra’ayi inji kakakin marasa rinjaye a majalis, Isuhu Issaka. Ya ce bara sun yi magana kada a yi wannan kuskuren. Sun yi amma yanzu « munji dadi » saboda za su koma kan matakan da suka ki da can.

Sakamakon rashin inganci layin waya hukumar saka ido akan ayyukan kamfanonin salula ARPT ta caji wadanan kamfanoni miliyan kusan 4000 na sefa, cfa, a shekarar 2017 a matsayin tara a sanadiyar koke koken masu amfani da wayar salula a nan Nijer.

A saurari rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG