Kawo yanzu Najeriya nada wakilci a kungiyoyin kasa da kasa har guda 310 lamarin da ya jawo mata basussuka na fiye da $120m.
A duk shekara Najeriya na kashe kudi kimanin $70m a ire-iren wadannan kungiyoyin.
Ministar Kudin Najeriya Femi Adeosun tace Najeriya zata fice daga kungiyoyi casa'in yayinda zata cigaba da kasancewa a sauran 220.
Dan Masanin Fika Alhaji Abba wanda ya taba zama shugaban daya daga cikin kungiyoyin, wato, kungiyar raya kogin Neja yana mai cewa kasashe tara ne suke cikin kungiyar amma rabin kudin aikin kungiyar Najeriya ce take samarwa. Idan Najeriya bata fita daga cikin irin kungiyar tafiyar da kogin Neja ba, zata cigaba da daukan nauyi. Bugu da kari Najeriya na cikin wasu kungiyoyi dake da alaka da kogin Neja.
Illar fita daga kungiyoyin zai yiwa Najeriya ya dangantaka ne da irin kungiyoyin da zata fita daga cikinsu inji Dr Kabiru Lawanti na Jami'ar Ahmadu Bello. Yana mai cewa akwai wadanda suke moran Najeriya saboda haka idan ta fita daga irin wadannan kungiyoyin babu wata illa. Inji Dr Lawanti wasu kungiyoyin ma basu da wani anfani da zasu yiwa kasar.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karinbayani.
Facebook Forum